A ranar 1 ga watan Afrilun nan, cibiyar binciken ayyukan samar da hidima ta hukumar kididdigar kasar Sin, da kwamitin kula da harkokin sayayya da jigilar kayayyaki na kasar Sin, sun fidda wani rahoto, inda suka bayyana cewa, a watan Maris, yawan alkaluman fihirarsar sayayya kasar Sin ya kai kashi 50.9 cikin 100, wato ke nan, adadin ya dade da tsawon rabin shekara yana kan sama da kashi 50 cikin 100, kuma ya karu da 0.8 cikin 100 bisa na watan da ya gabata.
Kwamitin kula harkokin sayayya da jigilar kayayyaki na kasar Sin ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, an fara farfado da cinikin kasuwanni, kuma an kara yin odar kayayyakin masana'antu da dama, kuma masana'antu na gudana yadda ya kamata, lamarin da ya haifar da karin bunkasar tattalin arzikin Sin ya zuwa mataki na gaba.(Bako)