in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba kamar yadda ake fata
2013-06-22 16:23:59 cri

A ranar Jumma'a 21 ga wata, Mr. Zhang Gaoli, mataimakin firaministan kasar Sin ya ce, yanzu tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba kamar yadda ake fata, kuma farashin kayayyaki bai tashi fiye da kima ba, har ma yawan mutane wadanda suka samu aikin yi ya karu. A waje daya kuma, ya nuna cewa, ko da yake tattalin arzikin kasar Sin na fama da wasu matsaloli da kalubale, duk da haka yana da wata kyakkyawar makoma.

Mr. Zhang ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi a yayin taron tattaunawar tattalin arziki kasa da kasa na karo na 17 da ake yi a birnin Saint Peterburg na kasar Rasha. Mr. Zhang ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma tabbatar da bunkasar tattalin arzikinta zai ba da muhimmiyar gudunmawa ga kokarin karuwar tattalin arzikin duk duniya. Don haka, kasar Sin za ta kara yin gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen duniya, ta yadda za a iya kara bunkasa masana'antu, kara bunkasa sana'o'in bayanai, kara mayar da yankunan karkara da su zama garuruwa da kuma shigo da fasahar zamani a aikin gona. Sannan za a kara bunkasa kasuwannin cikin gida, kara mai da hankali kan kyautata tsarin tattalin arziki, kare muhallin duniya, da kyautata rayuwar jama'a, ta yadda za a iya kyautata ingancin neman ci gaban tattalin arziki, da kuma neman ci gaba cikin lumana.

Zhang Gaoli ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan kare halaltacciyar moriyar masu zuba jari na kasashen waje domin kokarin bayar da kyakkyawar gudummawarta wajen farfadowa da kuma bunkasar tattalin arzikin duniya gaba daya.

A nasa bangaren kuma, Mr. Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha ya nuna cewa, kasar Rasha za ta kyautata tsarin tattalin arzikinta, da kara sa ido kan masana'antu, a kokarin kafa wani kyakkyawan muhallin jawo hankalin masu zuba jari na kasashen waje da su zuba jari a kasar Rasha cikin dogon lokaci mai zuwa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China