in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sa kyakkyawan fata ga makomar tattalin arzikin kasar Sin
2013-05-30 14:54:45 cri
Babban mataimakin shugaban asusun ba da lamuni na duniya IMF, Mr Lipton ya nuna a ran 29 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ko da yake, tattalin arzikin duniya na samun koma baya, amma karuwar tattalin arzikin kasar Sin bisa yadda aka kiyasta zai kai kimanin kashi 7.75 bisa dari.

Ban da haka, ya ce, an dan rage wannan adadi bisa na wanda aka kiyasta a baya, amma Sin na da makoma mai haske wajen samun bunkasuwar tattalin arziki.

Lipton ya yi wannan furuci ne a gun wani taron manema labarai da aka yi bayan tawagar IMF ta yi tattaunawa da jami'an kasar Sin kan manufar kasar ta hudu.

Lipton ya kara da cewa, yana farin ciki ganin cewa, Sin tana yin kwaskwarima a dukkan fannoni, da tabbatar da samun bunkasuwa cikin daidaito, har ma da samun bunkasuwar tattalin arziki bisa tsarin hakuri da juna da kiyaye muhalli.

Idan Sin ta samu nasara a wannan fanni, ba ita kadai ce za ta amfana ba, zai yi tasiri sosai a dukkan fadin duniya.

An ba da labari cewa, IMF ta kan yi tattaunawa da Amurka, Birtaniya, Sin, da kasashen da suke amfani da kudin Euro da Japan a ko wace shekara, abin da aka lakabin "Duba yanayin kasashe mafi girma a fannin tattalin arziki a ko wace shekara." (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China