An yi dandalin tattauna na kamfanoni mafi karfi 500 a fannin cinikayyar shige da fice na kasar Sin karo na 4 a kwanan baya a birnin Ningbo. Mai masaukin kungiyar kididdiga a fannin cinikayyar shige da fice ya gabatar da sunayen wadannan kamfanoni 500 a taron, ciki hadda kamfanin samar da man fetur na kasar Sin, kamfanin masana'antar man fetur na kasar Sin, kamfanin sadarwa na Huawei da dai sauransu wadanda yawan kudi da ko wanensu suka juya ya kai dala miliyan 723.
Bisa kididdigar da aka gabatar, yawan kudin da wadannan kamfanoni 500 suka juya a fannin cinikayyar shige da fice ya haura dala biliyan 1400 a bara, wanda ya kai kashi 36.35 cikin dari bisa dukan adadi a wannan fanni. Ko da yake sun dauki muhimmin mataki a wannan fanni, amma yawan kudin da wadannan kamfanoni suka juya ya ragu bisa dukan adadi na jimlar GDP, abin da ya dace da halin da ake ciki yanzu a wannan fanni. (Amina)