Hukumar da ke kimanta darajar kamfanoni a kasashen duniya wato Moody's, ta yi hasashen cewa, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin a kowace shekara za ta tsaya a kashi 7 zuwa 8 cikin dari har zuwa shekara ta 2017 ba tare da ya sauko kasa ba.
Hukumar ta ce, sabbin shugabannin kasar ta Sin, suna ciyar da manufar kasar da matakan gyare-gyare gaba yadda ya kamata, matakin da hukumar ta ce zai taimaka wajen magance faduwar kadarori da hana hauhawarsu.
Hukumar ta ce, alkaluman farashin kayayyakin da jama'a suke saya(CPI) wato ma'aunin da ke nuna mizanin hauhawar farashin kaya, shi ma ba zai tashi ba, kana an daidaita yiyuwar hauhawar farashin filaye da gidaje.
Bugu da kari, hukumar ta kuma sanya kasar Sin cikin mataki na Aa3, amma daidaituwar yanayin tsarin tattalin arzikin kasar a bangaren bashi a watan Afrilu yana matakin da ya dace, inda ta nuna damuwa game da karuwar bashin kananan hukumomi, karuwar bayar da bashin bankuna da rashin ci gaban matakan gyare-gyaren tattalin arziki.
Amma duk da wadannan matakai da kasar ke dauka, hakan ba zai wadatar ba wajen kimanta matsayin kasar nan zuwa watanni 12-18 masu zuwa.(Ibrahim)