Yayin taron manema labaran da aka yi dangane da yanayin makomar tattalin arzikin Sin, da ofishin ba da labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira, Wang Yiming ya nuna cewa, gyare-gyaren da Sin ke yi za su iya karfafa bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci, ta yadda lamarin zai ba da taimako mai yakini ga samun karuwar tattalin arzikin duk duniya cikin daidaici kuma mai dorewa.
Wang Yiming ya kuma kara da cewa, saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya dace da tsarin tattalin arziki, kuma a halin yanzu bunkasuwar karkarar biraren kasar Sin na da muhimmiyar ma'ana wajen bunkasa bukata cikin gida, hakan zai zama wani sabon karfin ingizawa domin raya tattalin arzikin kasar. (Maryam)