Li ya yi wannan tsokaci ne ranar Talata 16 ga watan nan, yayin da yake jawabi gaban mahalarta wani babban taron masu ruwa da tsaki kan nazarin halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, taron da ya biyo bayan wasu alkaluman kididdiga dake nuna cewa, kasar ta samu koma baya a fannin karuwar tattalin arziki da kaso 7.5 bisa dari daga watan Afrilu zuwa Yuni, maimakon kaso 7.7 bisa dari da aka samu a farkon watanni uku na shekarar nan ta 2013.
Masana da masu fashin baki dai na ganin tattalin arzikin kasar Sin na bisa turba ta gari, duk kuwa da kalubale, da kuma rashin tabbas da aka iya fuskanta.
A cewar Li, sauyi a fannin tattalin arziki abu ne da ba za a iya kauce masa ba, illa dai akwai bukatar daukar matakan kariya, domin dakile tazara mai yawa daka iya aukuwa a wannan fage, ta yadda za a ci gaba da samun ci gaban da ake fata. Ya ce Sin na burin ci gaba da daukar matakan kare ayyukan yi, da kuma kiyaye hauhawar farashin kayayyaki. A lokaci guda kuma ana fatan dorewar habakar tattalin arziki da kaso 7.5 bisa dari a bana, tare da tsaida alkaluman hauhawar farashin kaya kan mizanin kaso 3.5 bisa dari.
A wannan lokaci da tattalin arzikin kasar Sin ke shiga sabon matsayi, a cewar Firimiya Li, dole ne a dauki matakan da suka wajaba, wajen gudanar da sauye-suye, haka nan wajibi ne gwamnati ta sa kaimi wajen kafa tsare-tsare bisa ilimin kimiyya, wadanda zasu tabbatar da daidaito a fannin sauyin da kan shafi kasuwanni, tare da samar da kyakkyawan yanayin ci gaba. (Saminu)