Asusun na IMF ya kawo karshen yin shawarwari da kasar Sin kan aya ta hudu a kwanan baya, kuma ya bayar da rahoto dagane da shawarwarin a ranar, inda ya nuna cewa, Sin ta samu ci gaba sosai wajen samun daidaito a fannin tattalin arziki, amma tana ci gaba da fuskantar matsalar rashin samu isashen daidaito a cikin gida, kuma ba ta cimma cikakkiyar nasara ba wajen samun karuwar tattalin arziki ta hanyar habaka bukatun cikin gida da na waje. Aikin da za a sa gaba yanzu shi ne gaggauta sauya hanyar raya tattalin arzki, tuni sabuwar gwamantin kasar kuwa ta fitar da wasu manufofi kan wannan batu. (Amina)