Rahotanni na cewa, yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla, ta hada da batutuwan samar da kudin haraji na gata, da jadawalin gudanar da aikin shimfida bututan, da kuma fasahohin da za a yi amfani da su, da ma'aunin fasahohi da dai sauransu.
Gaba daya dai wannan harka ta shimfida bututan mai, za ta kai kilomita 1400, wanda bisa kasafin kudi da kasashen 2 suka yi, aikin zai lashe dalar Amurka biliyan 3.55, lamarin da ya sanya aikin kasancewa bututun man fetur mai aiki da lantarki mafi tsawo a duniya.
Aikin zai fara ne daga yankin Hoima na kasar Uganda, ya kuma kare a tashar jirgin ruwa ta Tanga dake kasar Tanzania. Kuma bisa shirin da aka yi, an riga an fara gina bututan a karshen shekarar 2016, yayin da za a kammala aikin a shekarar 2020.
Tuni dai aka gano man fetur sama da ganga biliyan 6.5 a yammacin kasar Uganda, wanda kuma ake fatan fara aikin hakar sa a yankin. (Maryam)