Sakataren yada labaran Jam'iyyar Humphrey Polepole, ya ce 'yan siyasa da 'yan kasuwa, na ikirarin cewa ana fuskantar karancin abinci a kasar domin cimma muradinsu na kashin kai.
Ya shaidawa wani taron manema labarai a Dar es Salam, babban birnin kasar cewa, jam'iyyun adawa ne ke kirkiro matsalar na karancin abinci, domin taimaka musu cimma muradinsu na siyasa.
Polepole ya yi kira ga jama'a su yi watsi da bayanai marasa sahihanci da shugabannin adawa ke yadawa game da yanayin abinci.
Ya kuma yi kira gare su, su mara baya ga ayyukan da gwamnati take da nufin inganta walwalarsu da habaka tattalin arziki. ( Fa'iza Mustapha)