Mashirya taron sun bayyana cewa, ana sa ran zai hada sassan jami'ai, da manoma, da kungiyoyin manoma, da kungiyoyi masu zaman kansu, da masu bincike. Sauran sun hada da 'yan kasuwa da masu zuba jari, da kuma bankuna.
Da yake tsokaci game da tasirin wannan taro, jami'in mai ba da shawarwari game da tsara manufofin inganta cinikayyar albarkatun gona, a ma'aikatar noma, da kiwo da kiwon kifi a Tanzania David Nyange, ya ce fasahohin da za a baje kolin su, za su taka muhimmiyar rawa, wajen zamanintar da cinikayyar albarkatun noma.
An dai fara gudanar da wannan baje koli ne shekaru 3 da suka gabata a birnin Chisamba, cibiyar noma ta kasar, bikin da tun daga wancan lokaci ya bude sabon shafi, a fannin bunkasa cinikayyar fasahohin noma da kiwo a daukacin bangarorin kasar. (Saminu Hassan)