Kungiyar kasuwanci ta kasar Sin dake kasar Uganda da hukumar zuba jari ta kasar Uganda suka gudanar da taron cikin hadin gwiwa, haka kuma, mataimakin shugaban kasar Uganda Edward Ssekandi, da wasu jami'an ma'aikatar harkokin kudi, da jakadan kasar Sin dake kasar Uganda Zheng Zhuqiang, da wasu wakilan kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu dake kasar Uganda sun halarci wannan taro.
A yayin taron, Mr.Ssekandi ya bayyana cewa, domin cimma burin kasar na 2024, a 'yan shekarun nan, kasar Uganda ta dukufa wajen raya ababen more rayuwa, a nan gaba kuma za ta mai da hankali kan raya harkokin masana'antu. Bugu da kari, kasarsa za ta ci gaba da kyautata yanayin zuba jari a kasar, da aiwatar da shirin hadin gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata, shi ya sa, kasar Uganda take fatan samun karin taimako da goyon baya daga bangaren kasar Sin domin karfafa bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar. (Maryam)