A ranar Lahadi da tsakar rana ne, dakarun tsaro su ka dira a fadar sarki Mumbere suka kuma kama shi, bayan kai ruwa rana da sojoji da 'yan sanda suka yi ranar Asabar da masu gadinsa.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Uganda Janar Jeje Odongo, ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa, ana tuhumar Mumbere ne saboda rawar da ya taka wajen haddasa tashin hankali.
Rahotanni na cewa, a kalla jami'an 'yan sanda 16 da dogarai 46 ne aka kashe a mummunan fadan da ya barke a karshen mako tsakanin dakarun tsaro da kabilun yankin da ke neman ballewa daga kasar da ke gabashin Afirka, domin kafa jamhuriyarsa ta Yiira, bayan da suka farma dakarun tsaro da ke sintiri a garin Kasese.(Ibrahim)