Jiya Litinin, firaministan kasar Tanzania Kassim Majaliwa ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar firaministan kasar dake birnin Dar es Salaam, a madadin shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli wanda a halin yanzu yake jagorantar ayyukan fuskantar bala'i a yanki mai nisa.
A yayin ganawar tasu, firaminista Majaliwa ya mika gaisuwar shugaba Magufuli ga shugaban kasar Sin Xi Jinping. Sa'an nan, ya ce, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa wajen raya kasar Tanzania, Tanzania tana fatan samun karin kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar, haka kuma, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kiyaye manufar kasar Sin daya tak, yayin goyon bayan kasar Sin kan harkokin dake shafar moriyarta.
A nasa bangare, Wang Yi ya nuna kyakkyawar fatan shugaba Xi Jinping ga shugaba Magufuli, inda yake sa ran ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma aiwatar da sakamakon taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata, da kuma tattaunawa kan kyautata layin dogo dake tsakanin Tanzania da Zambia, ta yadda za a ba da gudummawa kan bunkasuwar kasashen Tanzania da Zambia, har ma da kasashen Afirka baki daya. (Maryam)