A jiya ranar 11 ga wata, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a birnin Kampala dake kasar Uganda.
Museveni ya bayyana cewa, Sin dadadar abokiya ce ta kasar Uganda da ta kasashen Afirka, ta nuna goyon baya ga jama'ar kasashen Afirka a yayin da suka yi yaki da 'yan mulkin mallaka. Yanzu Sin ta samu ci gaba, ta kara nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, kasar Uganda ta nuna godiya ga kasar Sin. Yanzu kasar Uganda ta tabbatar da shirin raya kasa da gaggauta bunkasa masana'antu, kuma tana fatan Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya da samar da gudummawa gare ta. Sin ta kiyaye aiwatar da manufofin yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannonin ayyukan more rayuwa, zuba jari, mu'amalar al'adu da sauransu, wadanda za su taimakawa kasashen Afirka wajen samun bunkasuwa mai dorewa, kuma sun bambanta da manufofin da wasu kasashe suka gudanar na taimakawa kasashen Afirka ta hanyar bada tallafin kayayyaki, da sayar da kayyayaki.
A nasa bangare, Wang Yi ya nuna yabo ga kasar Uganda da ta tsara shirin raya masana'antu da aikin noma, ya bayyana cewa, Sin tana son zama abokiyar hadin gwiwa ta kasar Uganda yayin da take kokarin raya kasa, da samar da gudummawa gare ta wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta. Wang Yi ya bayyana cewa, Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Uganda a fannonin ayyukan more rayuwa da gina yankin masana'antu, da taimakawa kasar Uganda wajen raya makamashi da aikin noma, don sa kaimi ga kasar Uganda da ta kasance kasa ta farko da ta samu zamanintar da masana'antu da aikin noma a yankin kasashen da ba su dab da teku ba. (Zainab)