John Magufuli ya yi wannan kira ne lokacin da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yada zango a kasar, a kan hanyarsa ta zuwa birnin New Yorkn daga Kenya.
Shugaban ya ce rashin kwanciyar hankali a kasashen biyu na kara yawan 'yan gudun hijira dake kwarara kasar Tanzania da sauran kasahe makwafta, ya na mai cewa akwai bukatar samar da tsarin siyasa mai dorewa a kasashen.
Ministan harkokin wajen Tanzania Augustine Mahiga da ya gabatar da kiran ga Sakatare Janar na MDD, ya ce a matsayin kasarsa ta jagorar kungiyar kwancen kasashen gabashin Afrika, ta na da kyakkywar fata, la'akari da nasarorin da aka samu a shiga tsakanin rikicin Burundi da tsohon shugaban Tanzaniyar Benjamin Mkapa ya taimakawa samarwa, wanda kuma Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya jagoranta. (Fa'iza Mustapha)