Cikin wata sanarwa da aka raba ga kafafen yada labarai, Shuagaba Museveni ya ce kasashen yamma masu ra'ayin sassauci na ci gaba da tafka kurakurai ta hanyar neman kakabawa al'ummar duniya ra'ayinsu.
Ya ce wadannan ra'ayoyi sun shafi zaman takewar iyali da tsarin demokradiyya da luwadi da tattalin arziki da sauransu, al'amarin da ya ce na kawo rarrabuwar kawuna da rikici wajen magance al'amuran da suka shafi kasa da kasa.
Ya ce akwai batutuwa da ya kamata duniya ta mai da hankali kansu kamar ilimin zamani a fannin kimiyya da zamantakewa da karfafawa mata da cinikayya da yaki da masu tsatsauran ra'ayi da sauransu.
Ya ce ci gaba da sukar kasashen Rasha da Sin da masu sassaucin ra'ayin ke yi, ba zai haifar da da mai ido ba, yana mai cewa kasashen 2 sun himmantu wajen ragewa miliyoyin al'ummar Afrika radadin talauci.
Ya ce har ila yau, kasashen na taimakawa kasashen Afrika yaki da mulkin mallaka da mummanan tasirinsa. (Fa'iza Mustapha)