A cikin wani sakon da ya gabatar da yammacin jiya Asabar, shugaban na Tanzaniaya, ya bayyana hadarin a matsayin wani mummunan ibtila'i da ya shafi kasar baki daya.
Hukumomi a kasar sun bayyana cewa a kalla mutane 31, da suka hada da dalibai 'yan makaranta da malamasu uku ne, suka gamu da ajalinsu, yayin da motar makarantar dake dauke da su ta kauce hanya da sanyin safiyar Asabar din da ta gabata.
Hadarin dai ya rutsa da dalibai da malamai 3 na makarantar Lucky Vincent English Medium Primary School dake arewacin safari a yankin Arusha dake babbban birnin kasar Tanzaniyan.
Theresia Mahongo, kwamishinan gundumar Karatu, ya ce lamarin ya auku ne bayan da motar makaranta ta kauce hanyar inda ta koma hanyar Marera dake da tazarar kilomita 150 daga birnin na Arusha.
Charles Mkumbo, kwamandan 'yan sanda na shiyyar Arusha ya fada cewar, suna ci gaba da gudanar da bincike game da musabbabin faruwar hadari ko yana da nasaba da tangardar na'ura ko kuma kuskure ne daga bangaren matukin motar. (Ahmad Fagam)