An kammala taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya hanya daya" a kwanakin baya a nan birnin Beijing. Ministan kula da manyan ayyuka da sufuri da sadarwa na kasar Tanzania Makame Mbarawa wanda ya halarci taron, ya bayyana a jiya Talata cewa, an gudanar da dandalin tattaunawar cikin nasara, kuma kasar sa za ta koyi fasahohi daga dandalin tattaunawar, kana tana fatan kasar Sin za ta shiga aikin gina ayyukan more rayuwa a kasar Tanzania.
Mbarawa ya bayyana wa 'yan jarida a wannan rana cewa, yanzu haka kasar Tanzania ta riga ta tsara shirin gina manyan ayyukan more rayuwa, kamar babban layin dogo na kasar, da gyara mashigin teku na Dar es Salaam, da hanyoyin jiragen kasa dake tsakanin Tanzania da Zambia, da kuma wasu ayyukan gina filayen jiragen sama.
Ya kara da cewa, Sin tana da karfi da fasahohi na gina ayyukan more rayuwa, yana fatan kuma kasar za ta shiga aikin gina ayyukan more rayuwa a kasar Tanzania. (Zainab)