in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jami'in gwamnatin Uganda ya yaba ma kasar Sin kan matakinta na haramta safarar hauren giwaye
2017-02-05 13:08:52 cri
Wani jami'in hukumar kula da namun daji na kasar Uganda ya yabawa gwamnatin kasar Sin game da daukar matakin hana safarar hauren giwa, inda ya ce matakin yana da ma'ana sosai ga kokarin kare giwaye don magance bacewarsu daga doron kasa.

Edward Aasalo, darekta mai kula da yankunan kariya karkarshin hukumar kula da namun daji ta kasar Uganda, ya shedawa manema labaru a ranar Jumma'a da ta gabata cewa, matakin da kasar Sin ta dauka na hana safarar hauren giwaye zai kawo sauyin yanayi, domin idan an daina sayen kayan, to masu fataucin kayan za su kawo karshen ayyukansu.

A cewar Aasalo, giwaye sun kasance daya daga cikin namun daji masu muhimmanci da suke janyo hankalin masu yawon shakatawa na kasashe daban daban zuwa kasar Uganda, sai dai yadda ake farautar giwaye ya haifar da matsaloli ga kokarin gwamnatin kasar ke yi na kare dabbobin. Cikin shekarun baya, gwamnatin Uganda ta tsaurara matakan hana farautar giwaye tare da samun wasu nasarori.

A nata bangare, majalisar gudanarwar kasar Sin ta sanar da haramta sarrafa hauren giwaye gami da sayar da kayayyakin da aka yi su da hauren giwaye a kwanakin baya, kuma za a dauki mataki don kawo karshen ayyukan sarrafawa da sayar da kayayyakin ne kafin ranar 31 ga watan Disamban bana.(Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China