Bugu da kari, kakakin rundunar sojin Uganda Brig Richard Karemire, ya ce, kasarsa ta fara janye sojojinta daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, biyo bayan kawo karshen aikin neman shugaban kungiyar Lord's Resistance.
Jimilar sojoji 1,500 ne Kasar Uganda ta aike da su zuwa kasar Afirka ta Tsakiya, kuma a ranar 19 ga wata ne ta janye tawagar sojojin rukuni na daya, sannan, za ta janye raguwar tawagar sojojin kafin karshen watan Mayu mai zuwa.
Sai dai, Uganda ta ce, za ta ci gaba da ba da taimako ga kasar Afirka ta Tsakiya wajen yaki da kungiyar adawa ta Lord's Resistance ta hanyoyin da za su dace. (Maryam)