Firaministan kasar Sin ya jaddada matsayin goyon bayan manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda 2017-03-16 A jiya Laraba da safe ne, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan Beijing. A wani taron manema labaru da aka shirya bayan taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin tana da karfin rike ci babban matsakaicin karuwar tattalin arzikinta nan da dogon lokaci...
Kasar Sin za ta kara ba da gudummawa ga farfadowar tattalin azikin duniya, in ji jakadan Jamhuriyar kasar Kongo dake Sin 2017-03-13 Taron shekara shekara na NPC da na CPPCC dake gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya jawo hankalin mutane sosai kasancewarsu a matsayin wani batu mai matukar muhimmanci ga jama'ar kasar Sin. A ranar 9 ga wata ne, wakilin CRI ya tattauna da jakadan Jamhuriyar kasar Congo Brazaville da ke nan kasar Sin Mr. Daniel Owassa kan tarukan biyu, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara ba da babbar gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ma kafuwar sabon tsarin kasa da kasa.