in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da babban kundin tsarin dokar kare hakkin al'ummar kasar Sin
2017-03-15 10:01:29 cri
A yau Laraba ne, wakilan jama'ar kasar Sin dake halartar taron shekara-shekara na majalisar NPC na wannan karo suka zartas da babban kundi mai kunshe da tsarin dokar kare hakkin al'umma. Hakan na nufin an kammala aikin tsara kundin dokar kare hakkin al'umma a kasar.

Wakilan jama'ar kasar 2838 ne suka halarci bikin rufe taron majalisar NPC, wanda ya gudana a yau Laraba, inda aka jefa kuri'a kan kundin tsarin dokar kare hakkin al'ummar. Cikin wakilan jama'ar da suka kada kuri'a, 2782 sun jefa kuri'ar amincewa, yayin da 30 suka jefa kuri'ar kin amincewa, sai kuma 21 da suka janye daga jefa kuri'ar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China