Firaministan na Sin ya shaidawa taron manema labarai, bayan kammala taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar cewa, yanzu haka kasar Sin ta bullo da matakan daidaita tattalin arzikinta, da wadanda za su kara karfin masana'antu da sayar da kayayyakin da suke kera da bullo da sabbin hanyoyin da za su sanya tattalin arzikin kan turbar da ta dace.
Wani abin farin ciki a cewar Mr Li shi ne, a cikin shekaru 4 da suka gabata gwamnatin ta bullo da karin guraben ayyukan yi miliyan 50 a biranen kasar.
Ya kuma yarda cewa, ana fuskantar tarin kalubale da wahalhalu a yayin da ake aiwatar da gyare-gyare, amma ya kuma lashi takwabin kara yin gyaran fuskan kan matakan tafiyar da gwamnati domin magance yadda wasu ke amfani da mukamansu ta hanyar ba ta dace ba. (Ibrahim Yaya)