A lokacin da aka gudanar da tarukan shekara-shekara 2 wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC da na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC a kasar a bana, kafofin yada labaru na kasashen ketare sun sha ambato kasar Sin da kalamomin "Gudummowar da Sin ta bayar", "salon kasar Sin", "dabarar kasar Sin" da dai makamantansu, lamarin da ya nuna cewa, a idanun al'ummomin kasashen waje, kasar Sin tana sauke nauyin da ke wuyanta yadda ya kamata, kuma tana nuna karfin zuciya sosai.
Kwanakin baya, wasu shahararrun hukumomin binciken ra'ayoyin jama'a ta kasa da kasa kamar Gallup da Pew na kasar Amurka sun kaddamar da sakamakon binciken ra'ayoyin jama'a, wanda ke bayyana cewa, darajar kasar Sin a zukatan jama'ar kasa da kasa tana samun kyautatuwa.
Wadannan hukumomi suna ganin cewa, kyautatuwar darajar kasar Sin a duniya na da nasaba da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannonin bunkasar tattalin arziki, sabunta kimiyya da fasaha, yaki da kangin talauci da dai sauransu. (Tasallah Yuan)