in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara na NPC na bana
2017-03-15 19:38:10 cri

Yau Laraba ne aka rufe taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) karo na 12 a nan birnin Beijing, bayan rufe taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar (CPPCC) karo na 12 a ranar 13 ga wata, tarukan da aka shafe kwanaki fiye da goma ana gudanarwa, baya ga kulawa da suka samu daga wajen jama'ar kasar Sin, a hannu guda sun kuma jawo hankulan kafofin watsa labarai, da kwararru na kasashen ketare.

Alal hakika tarukan biyu wato na NPC da CPPCC muhimman lamuran siyasa ne na kasar Sin dake gudana a ko wace shekara, su ne kuma muhimmiyar hanyar da kasashen duniya ke dauka, ta sa ido ga yadda kasar Sin ke gudanar da harkokinta, da manufofin da take bi wajen gudanar da harkokin tattalin arziki da diplomasiyya, da yadda zaman rayuwar jama'a da al'adun suke a nan kasar.

A yayin da matsayin kasar Sin ke dada daukaka a duniya, kafofin watsa labaru, da jama'ar kasashen ketare, suna ta mayar da hankali kan wadannan taruka biyu na Sin.

Kwararre daga kasar Poland kan batun kasar Sin, kuma tsohon karamin jakadan kasar dake birnin Shanghai na Sin, mista Sylwester Szafarz, ya mai da hankali sosai kan burin karuwar tattalin arzikin da Sin ta tsara a bana, da kudin da za ta kasha a fannin aikin soja, da yin kwaskwarima ta bangaren samar da kayayyaki, da kuma wasu batutuwan da suka shafi kiyaye muhalli, da samar da gidaje da dai sauransu. A yayin da yake zantawa da majiyar mu ya bayyana cewa, wasu abubuwan da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar a cikin rahoton ayyukan gwamnati, ciki har da bunkasuwar tattalin arzikin kasar a matsayin kasha 6.7 cikin dari cikin shekarar 2016, da kyautata tsarin tattalin arziki da kirkire-kirkire a wannan fanni, da kuma bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, dukkansu sun burge shi sosai.

"Abin da ya fi burge ni shi ne, bayanan da firaministan Sin ya gabatar game da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Firaministan ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da yin kirkire-kirkire don inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, ciki har da saukaka yadda wasu masana'antun sarrafa kwal da karafa ke samar da kayayyaki fiye da kima, wannan yana da ma'ana kwarai, saboda hakan zai kawo cikas ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin. Baya ga haka, firaministan ya ce, kasar Sin za ta rage kayayyaki masu gurbata muhalli da masana'antu suke fitarwa, tare kuma da yin rigakafi da shawo kan gurbatar ruwa, kasa da kuma iska, wannan shi ma ya burge ni sosai."

Kasar Sin abokiyar cinikayya mafi girma ce ta kasar Australia. Ra'ayoyin bainal jama'a na kasar suna ganin cewa, rahoton ayyukan gwamnati da firaminista Li ya gabatar ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar zai ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata, hakan ya samar da bayanai masu kyau da ka iya amfanar Australia.

Shugaban sashen nazarin dangantaka tsakanin Australia da Sin na jami'ar UTS, kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar mista Bob Carr ya bayyana cewa, hasashen da Sin ta yi na samun karuwar tattalin arziki na kimanin kasha 6.5 cikin dari, zai samar da dama mai kyau da kasar sa:

"A gani na, labari mafi kyau ga Australia shi ne, karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba ya kai kaso 6.5 cikin dari, wannan ya ba mu kwarin gwiwa sosai. Saboda kamar yadda muka sani, yanzu haka kasar Sin na kyautata tsarin tattalin arzikinta, wato za a samar da kayayyaki domin biyan bukatu, amma ba domin zuba jari da fitar da kayayyakin masana'antun kere-kere a kasashe ketare kamar yadda aka yi a da ba."

Manufofin diplomasiyya da Sin ke bi, su ma na jawo hankulan kwararru na kasashen ketare. Kwararre daga kasar Poland mista Szafarz ya ce, ban da bayanan da aka gabatar a cikin rahoton ayyukan gwamnati, ya kuma mai da hankali kan bayyanan da firaminista Li Keqiang, da ministan harkokin waje Wang Yi suka gabatar, game da dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, da Sin da Amurka, da Sin da kungiyar ASEAN, da Sin da Afirka, da kuma Sin da Japan.

"Amsoshin da firaminista Li Keqiang da Mr. Wang Yi suka gabatar dukkansu sun jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matsayi na samun ci gaba ta hanyar lumana, da neman bunkasuwa mai cike da daidaito, da gudanar da hadin kai na samun moriyar juna, da kuma bunkasa dangantakar abokantaka tare da Turai da sauran kasashe."

A sa'i guda, mista Szafarz ya bayyana cewa, kasafin kudin da Sin za ta yi amfani da shi a fannin soja a shekarar 2017, ya kai kimanin kaso 7 cikin dari, wato ya yi kasa da kashi 10 cikin dari cikin shekaru biyu da suka wuce a jere, amma sauran kasashe ciki har da Amurka, suna kokarin kara kudin kasafin ayyukan soja, wannan ya nuna cewa, kasar Sin na fatan kawar da gardama cikin lumana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China