in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara ba da gudummawa ga farfadowar tattalin azikin duniya, in ji jakadan Jamhuriyar kasar Kongo dake Sin
2017-03-13 11:01:17 cri

Taron shekara shekara na NPC da na CPPCC dake gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya jawo hankalin mutane sosai kasancewarsu a matsayin wani batu mai matukar muhimmanci ga jama'ar kasar Sin. A ranar 9 ga wata ne, wakilin CRI ya tattauna da jakadan Jamhuriyar kasar Congo Brazaville da ke nan kasar Sin Mr. Daniel Owassa kan tarukan biyu, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara ba da babbar gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ma kafuwar sabon tsarin kasa da kasa.

Masu sauraro, shekarar 2017 shekara mai matukar muhimmanci cikin shirin raya kasa na 13 da kasar Sin kan tsara a ko wadannen shekaru biyar biyar, haka kuma shekara ce da za a karfafa aikin yin kwaskwarima ga tsarin samar da kayayyaki a dukkan fannoni. Yayin da Jakada Daniel Owassa ke ambatar batun da ya fi jawo hankalinsa a taron shekara shekara na NPC da na CPPCC na bana, ya bayyana cewa,

"A tarukan biyu na bana, akwai batutuwan da aka tattauna a kai da suka jawo hankalin mutane sosai, amma abin da ya fi burge ni shi ne kudurin da gwamnatin kasar Sin da ma jama'ar kasar ke nunawa wajen tunkarar matsaloli da kalubalolin da ke gabansu, musamman ma a fannonin kara karfin yaki da kangin talauci, tinkarar matsalar sauyin yanayi, da yaki da cin hanci da rashawa, gami da kiyaye bunkasuwar tattalin arziki."

Game da rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin da firaminista Li Keqiang ya gabatar a yayin bikin bude taron shekara shekara na NPC na bana, Jakada Daniel Owassa ya furta cewa,

"Rahoton aikin gwamnati da firaminista Li Keqiang ya gabatar ya kunshi abubuwa da yawa, kuma ana iya raba su zuwa kashi biyu, wato waiwayen aikin gwamnati na shekarar 2016, da kuma tsara shirin aiki na shekarar 2017. A shekarar 2016, jimillar GDP da kasar Sin ta samu ta karu da kashi 6.7 cikin dari bisa na shekarar 2015, a bana kuma, ana sa ran jimillar za ta iya karu da kashi 6.5 cikin dari. Wadannan alkaluma biyu ba ma kawai sun shaida amincewar da aka nuna wa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi a cikin shekarar da ta gabata ba, hatta ma ya nuna mana imanin da gwamnatin kasar Sin ke da shi wajen gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin kasar a wannan shekarar da muke ciki."

Kididdigar wata abin lallashi ne mafi kyau. Jakada Daniel Owassa na da imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ba ba babbar gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya. Yana mai cewa,

"Alkaluman GDP na shekarar 2016 da shekarar 2017 da muka ambata a baya, suna nuna cewa, babu wani bambanci mai girma a tsakaninsu, gaskiya gwamnatin kasar Sin ba ta tsara burin da ba za ta iya cimmawa ba. Amma a waje daya kuma, gwamnatin kasar Sin tana da imani wajen samun karuwar tattalin arzikinta yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, ya kamata mu lura da wata kididdiga, wato yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar a duniya ta fuskar karuwar tattalin arziki ya zarce kashi 30 cikin dari a shekarar bara. Don haka muna da imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai taimaka matuka wajen farfadowar tattalin arzikin duniya."

A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, firaminista Li Keqiang ya nuna cewa, kasar Sin za ta ba da sabuwar gudummawa ga aikin hade makomar bil Adam bai daya. A farkon wannan shekarar ce a babbar hedkwatar MDD da ke Geneva, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana hasashen "kafa makomar bil Adam ta bai daya", wanda ya burge Jakada Daniel Owassa sosai, yana ganin cewa, wannan hasashe na da ma'ana sosai ga aikin bullo da sabon tsarin kasa da kasa. Ya kara da cewa,

"A karshen karnin da ya gabata, halin da duniya ke ciki ya canja sosai, daga baya kuma aka kafa tsarin kasa da kasa da ake amfani da shi a halin yanzu. Amma a karni na 21 da ake ciki, dan Adam na fuskantar sabbin kalubaloli iri daban daban, kamar su ta'addanci, sauyawar yanayi da dai sauransu. Tabarbarewar tattalin arzikin duniya ma ya haifar mana barazana sosai. Ganin hakan, shugaba Xi Jinping ya gabatar da hasashe na 'kafa makomar bil Adam ta bai daya'. Yanzu duniya ta kasance tamkar wani kauye daya, inda kasashen duniya ke kara dogaro da juna, don haka wannan hasashe zai baiwa kasashe daban daban damar fahimtar barazanar da ke gaban dan Adam, sa'an nan su hada kansu don martaba ka'idojin duniya, ta yadda za a aiwatar da harkokin da suka shafi duniya yadda ya kamata." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China