in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jaddada matsayin goyon bayan manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda
2017-03-16 11:47:02 cri

A jiya Laraba da safe ne, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan Beijing. A wani taron manema labaru da aka shirya bayan taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin tana da karfin rike ci babban matsakaicin karuwar tattalin arzikinta nan da dogon lokaci, kuma za ta ci gaba da ba da karin gudummawa ga karuwar tattalin arzikin duk duniya. A yayin da wasu ke korafe-korafe game da manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, Li Keqiang ya jaddada matsayin kasar Sin game da kare wannan manufa, da nuna goyon baya ga yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci. Firaministan kasar Sin ya kuma nanata cewa, kasar Sin za ta goyi baya tare da daukar dukkan matakan da suka wajaba na ganin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda. Kasar Sin ta ce manufarta ta bude kofarta ga kasashen duniya za su taimaka ga dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda. Sabo da haka, ko da za a samu wanzuwar kalubale iri iri, manufar ba za ta magance kowace irin matsala da ta bijiro sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda ba.

A matsayinta na kasa ta biyu a mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana burin samun kaso 6.5 cikin 100 na karuwar tattalin arzikinta a bana. Li Keqiang yana mai cewa, wannan ba karamin buri ba ne.

"Idan kasar Sin za ta iya cimma wannan buri na karuwar tattalin arzikinta a bana, jimillar karuwar tattalin arzikinta za ta zarce ta bara sabo da jimillar tattalin arzikinmu a bara ta zarce kudin Sin RMB yuan biliyan dubu 74, kwatankwacin dalar Amurka biliyan dubu 11, sannan za a samar da sabbin guraben aikin yi fiye da miliyan 11 a bana. Wannan burin da ake fatan samu ya dace da yanayin gudanar tattalin arzikin kasar. Sa'an nan kasar za ta ci gaba da kasancewa babbar kasar dake ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya, duk da koma bayan yanayin tattalin arziki da kasashe daban daban na duniya ke fuskanta."

A waje daya, kasar Sin kasa ce dake da kudaden musaya mafi yawa a duk duniya. Sakamakon haka, Li Keqiang ya ce, yawan kudaden musaya da kasar Sin ke da su za su biya bukatun kayayyakin da za a shigo da su daga ketare da wasu basusukan gajeren lokaci da za ta mayar. Sannan, ya jaddada cewa, kasar ba za ta rage darajar takardar kudinta dan bunkasa harkar fitar da kayayyaki ba. kuma ba ta son shiga yakin cinikayya. Kasar Sin za ta yi kokarin rike darajar kudinta kamar yadda ya kamata.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi kiran da a daina hasashen da ake yi game da yanayin tattalin arzikin kasar. Yana mai cewa kasar Sin tana da karfin rike ci gaban babban matsakaicin tattalin arzikinta nan da dogon lokaci. Wani abin farin ciki a cewar Mr Li shi ne, a cikin shekaru 4 da suka gabata gwamnatin ta bullo da karin guraben ayyukan yi miliyan 50 a biranen kasar.

"Hakikanin abubuwan da suka faru a cikin 'yan shekarun baya sun shaida cewa, ya kamata a daina has ashen da ake yi game da "saukar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri fiye da kima". Tattalin arzikin kasar Sin ba zai sauka cikin sauri fiye da kima ba, kasar Sin tana da karfin rike ci babban matsakaicin ci gaban tattalin arzikinta nan da dogon lokaci, kuma tattalin arzikinta zai inganta."

Firaministan na Sin ya kuma yarda cewa, hadari mafi tsanani ga kasar Sin shi ne rashin samun ci gaba. Ya kara da cewa, ana fuskantar tarin kalubale da wahalhalu a yayin da ake aiwatar da gyare-gyare, amma kuma ya lashi takwabin kara yin gyaran fuskan kan matakan tafiyar da gwamnati domin magance yadda wasu ke amfani da mukamansu ta hanyar ba ta dace ba.

A 'yan watannin baya ne, wasu ke korafe-korafe game da manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda. A watan Janairun bana, a yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na dandalin Davos, Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, kasar Sin za ta yi kokarin kare wannan manufa, tare da nuna goyon baya ga ciniki da zuba jari cikin 'yanci. Kuma za ta saukaka sharudan yin cinikayya da zuba jari, a lokacin da take ci gaba da bude kofarta ga kasashen duniya, shugaba Xi Jinping ya fito karara yana nuna adawa da matakan nuna kariya ga harkokin cinikayya. A jiya, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya maimaita wa 'yan jaridun gida da na waje wannan matsayin da kasar Sin take dauka. Ya jaddada cewa, "Kamar yadda sauran kasashen duniya suka amfana, kasar Sin ma ta ci gajiya sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda. Wani dalili kuma shi ne kasar Sin ta dade tana tsayawa tsayin daka wajen bin manufar bude kofarta ga sauran kasashen duniya. Da farko dai, kasar Sin za ta daidaita harkokinta kamar yadda ake fata, amma idan ta rufe kofarta, hakan ba zai taimaka mata wajen daidaita harkokinta kamar yadda ake fata ba. Sakamakon haka, za mu kara bude kofarmu ga daukacin kasashen duniya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China