Firaministan Sin: kasar Sin za ta ci gaba da ciyar da tattalin arzikin duniya gaba
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya furta a yau Laraba cewa, burin da kasar Sin ta sanya a gaba na kaso 6.5 cikin 100 na karuwar tattalin arzikinta a bana ba karamin buri ba ne, domin yawan kudin tattalin arzikin kasar ya riga ya zarce dalar Amurka biliyan dubu 11. A cewarsa, wannan burin da ake fatan samu ya dace da yanayin gudanar tattalin arzikin kasar. Sa'an nan kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa babbar kasar dake ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duk duniya, a yayin da ake fuskantar yanayin koma bayan tattalin arziki a kasashe daban daban na duniya.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku