in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
• Firaministan kasar Sin ya jaddada matsayin goyon bayan manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda 2017-03-16
A jiya Laraba da safe ne, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan Beijing. A wani taron manema labaru da aka shirya bayan taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin tana da karfin rike ci babban matsakaicin karuwar tattalin arzikinta nan da dogon lokaci...
• An rufe taron shekara-shekara na NPC na bana 2017-03-15
• Kasar Sin za ta kara ba da gudummawa ga farfadowar tattalin azikin duniya, in ji jakadan Jamhuriyar kasar Kongo dake Sin 2017-03-13
Taron shekara shekara na NPC da na CPPCC dake gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya jawo hankalin mutane sosai kasancewarsu a matsayin wani batu mai matukar muhimmanci ga jama'ar kasar Sin. A ranar 9 ga wata ne, wakilin CRI ya tattauna da jakadan Jamhuriyar kasar Congo Brazaville da ke nan kasar Sin Mr. Daniel Owassa kan tarukan biyu, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara ba da babbar gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ma kafuwar sabon tsarin kasa da kasa.
• An samu ci gaba ta fuskar kyautata ingancin iska a kasar Sin 2017-03-10
An gudanar da taron manema labarai a jiya Alhamis da yamma, bisa agogon Beijing, dangane da taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da ke gudana a nan birnin Beijing, inda ministan kiyaye muhalli na kasar, Chen Jining ya bayyana cewa, tun bayan da aka aiwatar da shirin magance gurbacewar iska, an samu kyakkyawan ci gaba ta fannin kyautata ingancin iska, ya kuma kara da cewa, ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar za ta kara karfin hana ayyukan gurbata muhalli, kuma ko kadan ba za a yi hakuri ga ayyukan da suka lalata muhalli ba.
• Xi Jinping ya tattauna da wakilan jama'ar kasar Sin kan batun fama da talauci 2017-03-09
A safiyar jiya Laraba, ranar 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kana shugaban kwamitin tsakiya na rundunar sojojin kasar, ya tattauna da wakilan lardin Sichuan, a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar NPC da ke gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
• Ministan harkokin wajen Sin ya yi bayani kan manufofin diflomasiyyar kasar Sin 2017-03-08
A yayin taron manema labarai da aka yi a yau Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani kan batutuwan dake janyo hankulan kasashen duniya, kamar hadin gwiwar kasa da kasa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, yanayin zirin Koriya da kuma manufofin diflomasiyyar kasar Sin da dai sauransu.
• Ra'ayin mai sauraronmu Ali Kiragi kan taron NPC da na CPPCC na kasar Sin 2017-03-07
A game da manyan tarukan biyu da a yanzu haka ke gudana a birnin Beijing, wato taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar(CPPCC), kwanan nan, wakiliyarmu a Abuja, tarayyar Nijeriya, Amina ta tattauna da wasu masu sauraronmu a kasar dangane da ra'ayoyinsu a kan tarukan, inda Ali Kiraji, wanda ya fito daga Yobe Nijeriya, ya bayyana ra'ayinsa kan yadda kasar Sin ke daukar matakai wajen fama da kangin talauci.
• Sin: rahoton aikin gwamnati ya dora muhimmaci kan kyautata zaman rayuwar jama'a 2017-03-07
Yayin da ake gudanar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wakilai kimanin 3000 dake cikin majalisar suna kokarin tantance shirin aikin da gwamnatin kasar ta gabatar. Abokin aiki Bello Wang na dauke da karin bayani dangane da batun.
• An duba rahoton aikin gwamnatin kasar Sin 2017-03-06
A jiya Lahadi 5 ga watan nan ne aka kaddamar da taron shekara shekara, na majalisar wakilan kasar Sin na bana a nan birnin Beijing. Yayin taron, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnatin kasar, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana kokarin cimma burin tabbatar da nufin karuwar GDP da kaso 6.5 bisa dari a shekarar bana da muke ciki, kana za a kara samar da guraben aikin yi sama da miliyan 11 a garuruwan kasar. Ban da haka kuma, za a kayyade adadin mutanen da suke rasa aikin yi zuwa kasa da kaso 4.5 bisa dari.
• Gwamnatin Sin ta yi bayani kan yadda za ta aiwatar da ayyukanta a shekarar 2017 2017-03-05
Yau Lahadi da safe, an kaddamar da cikakken zaman taro na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC karo na 12, inda aka yi bayani kan yadda gwamnatin kasar za ta aiwatar da ayyukanta a bana.
• An bude taron majalisar CPPCC a kasar Sin  2017-03-03
A yau Jumma'a ne aka bude taro na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC ta 12, a nan birnin Beijing.
• Za a kaddamar da taron CPPCC na bana a Beijing 2017-03-03
A yau Jumma'a 3 ga wata da yamma, agogon kasar Sin, za a kaddamar da taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC na bana a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, hakan ya alamanta cewa, za a fara gudanar da taruka biyu na kasar Sin wato taron majalisar wakilan kasar da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, wadanda ke jawo hankalin jama'a a hukumance. A yammacin jiya Alhamis ne, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kira taron manema labarai, inda kakakin watsa labarai na taron majalisar Wang Guoqing ya bayyana a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai cewa, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba yadda ya kamata, kuma zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China