Da yake jawabi ga taron manema labarai bayan kammala zaman majalisar dokokin kasar na shekara-shekara a yau Laraba, Li Keqiang ya ce tuni ofisoshin jakadancin kasashen biyu suka fara tattaunawa game da ganawar gaba da gaba da shugabannin biyu za su yi.
Ya ce dangantaka tsakanin Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, ba kadai ga kasashen ba, har ma da yankunansu da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali na duniya baki daya.
A don haka, ya ce dole su yi aiki tare wajen inganta wadannan abubuwa. (Fa'iza Mustapha)