in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kara samun gurbatacciyar iska a Afirka
2016-10-25 10:56:06 cri
Kwanan baya, kungiyar hadin gwiwa da raya tattalin arziki ta OECD ta fidda wani rahoto da ke nuna cewa, a halin yanzu, matsalar gurbatacciyar iska ta kasance babbar kalubale ga lafiyar al'ummomin kasashen Afirka, har ma tana haddasa asara kimanin dallar Amurka biliyan 450 a ko wace shekara a bangaren tattalin arzikin nahiyar Afirka. Babban dalilin da ke kawo wannan matsala shi ne saurin bunkasuwar birane a fadin nahiyar.

Ya zuwa shekarar 2050, adadin mutane a nahiyar Afirka zai karu zuwa biliyan 2.5, adadin da zai kai kashi 25 bisa dari na al'ummar duniya. Ana ganin matsalar gurbatacciyar iska tana iya haddasa karin barazana ga lafiyar al'ummomin nahiyar, baya ga matsalar sauyin yanayi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China