in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gama aikin taimakawa kasashen Afirka a fannin yin hasashen yanayi a karshen bana
2016-06-18 13:11:19 cri

Shugaban hukumar kula da harkokin yanayi ta kasar Sin Zheng Guoguang dake halartar taron majalisar gudanarwar ta hukumar yanayi ta duniya a birnin Geneva ya kira taron manema labaru a jiya ranar 17 ga wata, inda ya yi bayani game da halin gudanar da aikin taimakawa kasashen Afirka a fannin yin hasashen yanayi na kasar Sin, ya ce za a gama dukkan aikin ga kasashe 7 a karshen bana.

Don aiwatar da ayyukan da aka cimma a gun taron ministoci karo na 5 na dandanlin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a watan Yuli na shekarar 2012 a birnin Beijing na kasar Sin, hukumar yanayi ta kasar Sin ta tsaida kudurin gina cibiyoyin yin hasashen yanayi a kasashe 7 na Afirka wato Comoros, Zimbabwe, Kenya, Namibia, Congo Kinshasa, Kamaru da Sudan don kara karfinsu na yin hasashen yanayi da bada hidima da yin rigakafi a wannan fanni.

Zheng Guoguang ya bayyana cewa, gudanar da aikin taimakawa kasashen Afirka a fannin yin hasashen yanayi zai kara karfin hukumomin yanayi na kasashen da suka samu taimakon, kana batun ya shaida cewa, Sin ta bada gudummawa ga sha'anin binciken yanayi na duniya.

Shugaban hukumar yanayi ta duniya David Grimes da babban sakataren hukumar Petteri Taalas da kuma shugaban sashen Afirka na hukumar sun yi jawabi bi da bi, inda suka nuna yabo ga irin aikin da Sin ta gudanar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China