Mr Solheim ya bayyana cewa, a watan Satumban bana ne, manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, da suka hada da Sin da Amurka suka amince da yarjejeniyar ta Paris, wannan ya taimaka wajen fara aiwatar da yarjejeniyar. A cewarsa, kasar Sin tana kokarin daukar matakai ba tare da gurbata yanayi ba wajen magance matsalar sauyin yanayi da gurbata muhalli, da taimakawa wajen samar da ayyukan yi da samun bunkasuwar tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, wannan mataki ne da ya kamata sauran kasashen duniya su yi koyi.
Mr Solheim ya ce, kasar Sin ta yi kira da aiwatar da tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da samar da gudummawa da yada fasahohi, da samar da fasahohi ga yankin Afirka dake kudu da hamadar Sahara da kasashe masu tasowa dake dab da yankin. Yana fatan kasar Sin za ta kara taimakawa yaduwar fasahohin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. (Zainab)