Haq ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, yanzu haka babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya gayyaci shugabannin kasa da kasa da su halarci bikin amincewa ko karba ko kuma shiga yarjejeniyar ta Paris. A cikin wasikar gayyatar, Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta kammala matakan amincewa da yarjejeniyar Paris din kafin karshen wannan shekara.
Haq ya bayyana cewa, wannan bikin zai baiwa sauran kasashen duniya damar shiga ko amincewa da yarjejeniyar ta Paris kafin karshen shekarar bana.
Ya zuwa yanzu, kasashe 19 ne suka kammala matakin amincewa ko shiga wannan yarjejeniya. Wasu kasashe ciki har da Sin da Amurka sun bayyana aniyarsu ta shiga yarjejeniyar kafin karshen wannan shekara. Sin za ta kammala dukkan matakan shiga yarjejeniyar kafin a gudanar da taron kolin kungiyar G20 da za a gudanar a birnin Hanzhou na kasar Sin a watan Satumba. (Zainab)