in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi
2016-09-30 10:44:41 cri

Kwana baya gwamnatin Nijar ta sanar da amincewa game da shirin doka na rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris ta shekarar 2015 kan sauyin yanayi, da kasar Nijar ta sanya wa hannu a ranar 22 ga watan Afrilun shekarar 2016. Kuma za a tura kundin gaban 'yan majalisar dokokin kasar domin samun amincewa.

An rattana hannu kan wannan yarjejeniya a ranar 12 ga watan Disamban shekarar 2015 a yayin taron MDD kan sauyin yanayi, da aka gudanar a birnin Paris. Inda yarjejeniyar ta bukaci dukkan bangarorin da suka rattaba hannu da su takaita fitar da abubuwa masu dumama yanayi kasa da digiri 2, da kuma da ci gaba da yin kokari wajen rage wannan karuwa zuwa digiri 1,5.

Wannan babban muradi zai bukaci wata niyya mai karfi ta kasashen duniya, da kuma wasu daruruwan biliyoyin dalar Amurka domin tabbatar da sauyi zuwa makamashi mai tsabta. Domin fara aiki, yarjejeniyar Paris sai ta samu amincewa daga a kalla kasashe 55 dake wakiltar kashi 55 cikin 100 na fitar da iska mai gurbata muhalli. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China