Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon, ya ba da sanarwa a jiya Jumma'a cewa, ya yi maraba da irin rawar da kasar Sin ke takawa wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya game da batun sauyin yanayi.
A ta bakin Stephane Dujarric, mai Magana da yawun babban sakataren ya ce, Ban ya yi maraba da kokarin da kasar Sin ta yi wajen ingiza kasashe membobin kungiyar G20 cimma sanarwar da ta shafi sauyin yanayi, kasancewarta kasar da ta karbi bakuncin taron..
A cewarsa, hakan ya shaida cewa, kasashen G20 na nuna goyon baya ga yarjejeniyar Paris, inda ake sa ran kasashen kungiyar zasu rattaba hannu a ranar 22 ga wannan wata a helkwatar MDD dake New York, wacce aka gabatar tun a wajen taron kolin na kasashen duniya kan sauyin yanayi a birnin Paris.
Bugu da kari, Ban Ki-Moon ya godewa kasar Sin wajen ba da jagoranci kan aikin ingiza hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya don tinkarar sauyin yanayi.
An gudanar da taron na masu daidaitawa na G20 karo na 2, daga ranar 6 zuwa ranar 8 ga watan nan a birnin Guangzhou na kasar Sin. A matsayinta na kasar da ta karbi bakuncin taron, kasar Sin ta shawarci mambobin kungiyar da su bayar da sanarwa a kan batun sauyin yanayi, tare da tabbatar da yarjejeniyar Paris..(Lami)