Ana sa ran kasashen duniya 130 ne za su rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris mai cike da tarihi a ranar 22 ga wannan watan na Aprilu.
Mai Magana da yawun MDD Farhan Haq, ya fada cewar, sama da kasashen duniyar 130 suka tabbatar da aniyarsu ta sanya hannu kan yarjejeniyar game sauyin yanayi, tun a wata Disambar shekarar da ta gabata ne aka gabatar da kudurin, a yayin babban taron kasashen duniya game da sauyin yanayi a birnin Paris.
Sama da shugabannin kasashen duniya 60 za su halarci bikin wanda za'a gudanar a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka.
Sakataren janar na MDD Ban Ki-moon, ya jaddada aniyar ci gaba da janyo hankulan kasashen duniya game da alfanun dake tattare da amincewa da yarjejeniyar ta birnin Paris.
Yarjejeniyar ta Paris ta ayyana bukatar rage dumamar yanayi daga kasa da maki biyu na ma'aunin Celsius zuwa kasa da maki 1 da digo 5.
Sannan ana sa ran manyan kasashen duniya za su tattara kudade da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 100 nan da shekara ta 2020, domin tallafawa kasashe masu tasowa wajen bunkasa tattalin arzikinsu.(Ahmad)