Ya zuwa shekarar 2050, yawan kudin da kasashe masu tasowa za su yi amfani da su wajen tinkarar sauyin yanayi zai karu zuwa dalar Amurka biliyan 280 ko dala biliyan 500 a ko wace shekara, kididdigar ta ninka sau 4 zuwa 5 bisa hasashen da aka yi a baya.
A saboda haka, kasashe masu tasowa za su fuskanci babban gibin kudi game da tinkarar matsalar sauyin yanayi.
Saboda haka, UNFCCC ta yi kira ga kasashe masu ci gaba da su samar da kudi dalar Amurka biliyan 100 a ko wace shekara har zuwa shekarar 2020, domin tallafawa kasashe masu tasowa wajen sassauta matsalar sauyin yanayi, ta yadda zai dace da tasirin da matsalar ta haifar, ciki har da bala'in fari, karuwar tsayin leburin teku da kuma bala'in ambaliyar ruwa da dai sauransu. (Bilkisu)