Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya zuwa yanzu, kasashe 60 na duniya sun mika takardar zartaswa ta yarjejeniyar Paris, don haka ya yi imanin cewa za a kai ga tabbatar da wannan yarjejeniya kafin karshen wannan shekara.
A game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang, ya bayyana a yau Alhamis a birnin Beijing cewa, kasar Sin tana maraba da karin kasashe da su amince su shiga yarjejeniyar, domin a fara aiki da yarjejeniyar tun da wuri.
Mr. Lu ya kara da cewa, sauyin yanayi kalubale ne da bil Adam baki daya ke fuskanta, kuma ya kamata kasashe daban daban su hada kan juna wajen tinkararsa. A matsayin babbar kasa mai tasowa dake kokarin sauke nauyin dake wuyanta, kasar Sin ta shiga yunkurin tinkarar sauyawar yanayi tare da kasashe daban daban, kana ta ba da gudummawa sosai wajen cimma yarjejeniyar Paris. Bugu da kari a kwanan baya, kasar ta Sin ta mika takardar zartaswa ta shiga yarjejeniyar Paris ga MDD a hukunce, matakin da ya kasance sabon alkawarin da ta dauka.(Lami)