Za'a gudanar da taron ne daga ranar 28 zuwa 30 ga wannan watan na Yuni, kana za'a yi nazari da kuma tattaunawa game da hanyoyin da za'a samar da cigaba mai dorewa a nahiyar.
Mahalarta taron na wannan shekara, za kuma su tabo batu game da yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da hukumomi masu zaman kansu don tara kudaden aiwatar da shirin takaita amfani da makamashi mai gurbata muhalli don samun cigaba.
Da yake zantawa da manema labarai a jiya Asabar, Vincent Biruta, minsitan albarkatun kasar Rwanda, yace kasar sa a shirye take ta karbi bakuncin taron wanda ake saran za'a tattauna yadda za'a shawo kan kalubale game da sauyin yanayi a nahiyar Afrika.