Kasashen Sin da Amurka sun mika takardar zartas da yarjejeniyar Paris ga MDD a jiya Asabar, hakan ya sa yawan kasashen da suka zartas da yarjejeniyar ya karu zuwa 26. Kungiyoyin kasa da kasa da kuma manyan kafofin watsa labaru na duniya sun nuna jinjina game da wannan mataki, suna ganin cewa abin da kasashen Sin da Amurka suka yi, ya baiwa al'ummar duniya kwarin gwiwa game da batun tinkarar sauyin yanayi.
Hukumar kula da harkokin muhalli ta MDD ta ba da sanarwa a jiya Asabar cewa, kasashen Sin da Amurka sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da yarjejeniyar Paris. A matsayinsu na manyan kasashe a fannin tattalin arziki, Sin da Amurka sun nuna wa duniya cewa, za a iya raya tattalin arziki ta hanyar kiyaye muhalli a nan gaba.
Sakataren gudanarwa na ofishin yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta MDD Patricia Espinosa Cantellano, ya ba da sanarwa a jiya Asabar cewa, ya nuna godiya ga kasashen Sin da Amurka wajen zartas da yarjejeniyar Paris, yana ganin cewa, hakan zai ingiza samun bunkasuwa mai dorewa a duniya. (Lami)