in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika guda bakwai sun samun tallafin kudi domin fuskantar matsalar sauyin yanayi
2016-08-13 14:19:57 cri
Kasashen nahiyar Afrika guda bakwai sun amfana da wani shirin shiyya da ya shafi taimakawa manoma domin fuskantar matsalar sauyin yanayi, a cewar wasu majiyoyi masu tushe a ranar Jumma'a a birnin Cotonou na kasar Benin.

Wannan shirin da aka taken "Tallafawa sauyi zuwa wani noma da tsare tsaren abince dake tafiya da ilimi bisa ga sauyin yanayi" zai amfanawa kasashen Benin, Cote d'Ivoire, Habasha, Gambiya, Ghana, Nijar da kuma Zambiya.

Bisa tallafin Norvege, shirin zai taimaka kasashen samun tallafin kudi sosai da dabarun zuba kudi ga sauyin yanayi ta hanyar tsare tsare na cikin gida da na shiyya shiyya da zuba jarin tafiya daidai da sauyin yanayi, in ji mista Tiemoko Yole, wakilin kungiyar noma da abinci ta MDD (FAO) dake kasar Benin.

Haka kuma, shirin zai taimaka wajen karfafa dangantaka tsakanin hukumomin bincike da shugabannin siyasa domin bunkasa fasahohin da suka dace ga noman dake tafiya da ilimi bisa ga sauyin yanayi (AIC), da kuma baiwa kasashe mambobi gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) damar kara saninsu kan AIC.

A cewar mista Yole, manufar AIC na tsakiyar wannan shirin, kungiyar FAO ta bunkasa shi da gabatar da shi a karon farko a dandalin tsaron cimaka da sauyin yanayi da ya gudana a birnin Haye a shekarar 2010.

Wakilin na FAO ya tunatar da cewa shirin za a aiwatar da shi cikin wani yanayi na kasa da kasa dake cike da niyyar gamayyar kasa da kasa wajen rage fitar da iska mai gurbata yanayi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris a yayin taron COP21 a cikin watan Disamban da ya gabata.

A cewar wasu hasashe, yammacin Afrika zai kasance daya daga cikin yankunan da zasu fama da sauyin yanayi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China