in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na son hada kai da sassa daban daban wajen aiwatar da yarjejeniyar Paris
2016-10-10 19:51:19 cri

A yau Litinin 10 ga wata ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa wadda ke sauke nauyin dake wuyan ta yadda ya kamata, kasar Sin na daukar matakan a-zo-a-gani na tinkarar kalubalen sauyin yanayi, ta kuma ba da kyakkyawar gudummowa wajen cimma daidaito kan yarjejeniyar Paris, wadda kuma za ta fara aiki nan gaba kadan.

Ya ce kasar Sin tana fatan hada kai da sassa daban daban wajen aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, tare da kara azamar gudanar da shawarwarin da ka iya biyo bayan fara aiki da yarjejeniyar.

An labarta cewa, a kwanan baya, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya sanar da cewa yarjejeniyar Paris za ta fara aiki ne a hukumance, tun daga ranar 4 ga watan Nuwambar bana. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China