Kaza lika, ya ce, cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Congo Brazzaville za ta ci gaba da karfafa ayyukan samar da ababen more rayuwa, da kuma daukar matakai yadda ya kamata domin raya tattalin arzikin kasar bisa fannoni daban daban, da kyautata ayyukan kiwon lafiya a kasar, haka kuma, ya ce, za a fara ba da horo ga matasa kan wasu fasahohi domin taimaka musu wajen neman ayyukan yi, samar da karin guraben aikin yi a kasar da kuma kara karfin al'ummomin kasar wajen yin cinikayya.
Ministan harkokin gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Chen Zhenggao ya halarci bikin rantsuwar da aka yi a birnin Brazzaville, a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin.
Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, Denis Sassou Nguesso ya lashe babban zaben ne da kashi 60.39 cikin 100 na kuri'un da aka kada a ranar 20 ga watan Maris, kuma wannan shi ne karo na biyu da ya lashe babban zaben shugaban kasar. (Maryam)