A nasa bangare shugaba N'Guesso wanda ke jawabi ga mane ma labarai bayan bayyana sakamakon, ya ce hakan ya nuna burin 'yan kasar, na shiga sabuwar janhuriyar ci gaba.
Shugaba N'Guesso, mai shekaru 72 da haihuwa, zai fara sabon zangon mulki na shekaru 5 masu zuwa, biyowa bayan lashe zaben ranar Asabar din da ta gabata. Ya kuma fara mulkin janhuriyar Congo ne shekaru 32 da suka gabata.
Bisa doka kotun tsarin mulkin kasar ce ke da hurumin tabbatar da sakamakon zaben. (Saminu Alhassan)