A cewar hukumomin kasar, wasu mayakan sa kai na Ninja Nsiloulou suka kai ma sojojin gwamnati hari wanda ake zaton sun shigo ta kudancin Brazzaville, ta unguwar Mayanga, dake yankin na 8 na Madilou.
Sun kai hari kan sojojin gwamnati dake Mayanga, kana ofishin 'yan sandar tsakiya na Djoue, ofishin 'yan sanda na yanki na 1 na Makelekele, da kuma ofisoshin 'yan sanda na unguwannin Lemira da Kinsoundi, dukkan wadannan gine gine tare da ofshin magajin garin Makelekele, an kona su, lamarin da ke kama da wani babban aikin ta'addanci, in ji mista Thierry Moungalla kakakin gwamnatin Congo. (Maman Ada)