in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta janye tawagar dakarun Congo dake Afrika ta Tsakiya
2016-01-10 14:23:54 cri
MDD ta yanke shawarar janye rukunin dakarun wanzar da zaman lafiya na Congo da aka tura cikin tawagarta dake Afrika ta Tsakiya (Minusca).

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Jumma'a, kakakin MDD, Stephane Dujarric ya tabo matsalar rashin taka rawar azo a gani na tawagar RDC.

Dakarun RDC-Congo sun samu nasarori amma wadannan dakaru basu amsa wasu bukatu kamar yadda MDD take so musamman ma a bangaren kayayyakin aiki, kulawa da daukar soja da kuma matsayin shiryawa a fagen yaki, in ji mista Stephane.

A cikin sanarwar, kakakin MDD ya bayyana cewa rukunin RDC, na kunshe da sojoji 807 da kuma 'yan sanda 118, ba za a maye gurbinsa ba idan ya janye daga cikin tawagar. A birnin Kinshasa, hukumomin kasar basu ce kome ba, game da wannan mataki na MDD.

A shekarar da ta gabata, rukunin RDC an zarge shi a cikin tawagar ta MDD da aikata fyade kan kananan yara.

Cibiyar MDD ta bukaci hukumomin Congo dasu gudanar da bincike kan sojojin da wannan zargi ya shafa. Saidai kuma hukumomin na Congo na ganin wannan wata makarkakashiya ce, kuma zargi ne wanda ba ya da tushe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China