in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan sa kai sun mamaye kauyuka da dama a gabashin RDC-Congo
2016-01-03 12:50:01 cri
Kimanin kauyuka tara ne mayakan sa kai suka karbe a baya bayan nan a yankunan Kalehe a kudancin Kivu, dake gabashin jamhuriyar demokuradiyyar Congo (RDC-Congo), a cewar wasu majiyoyin soja.

Majiyoyin rundunar sojojin RDC-Congo na FARDC sun bayyana cewa wadannan mayakan sa kai da suka mamaye wadannan kauyuka suna nan suna aikata miyagun laifuffuka kan fararen hula, musammun ma karbe dukiyoyin jama'a da kuma tsare mutane ba bisa doka ba.

Daga cikin shugabannin dakarun, a cewar majiyoyin kungiyoyin fararen hula na wurin, akwai Bwale Hamakombo, Tumaini Kapitwa, Gyeme Munomo, Masahani da Mungoro Matofali, dake ikonsu a wadannan kauyuka.

A cewar majiyoyin, wadannan shugabannin mayakan, yawancinsu 'yan kabilar Raia Mutomboki ne, kuma daga cikinsu biyar sun kafa sansanoninsu a Mushenge da Ekingi a cikin yankin Kalehe na kudancin Kivu.

Hukumomin wadannan yankuna da jihohi sun tabbatar da wadannan bayanai na mamaye kauyukan tare da bayyana cewa an fara kaddamar da ayyukan soja domin korar maharan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China