A bangaren MDD, karara ne cewa muna fatan shirin zabe yayi la'akari da wa'adin kundin tsarin mulki, in ji Charles Antoine Bambara, darektan watsa labarai na Monusco.
A ganin mista Bambara, akwai bukata na gudanar da tattaunawa da za ta iya bada damar cimma wani jadawali da za a yi amfani da shi a ranaku masu zuwa.
Ina ganin wannan yana da muhimmaci sosai. Kuma yanzu, gaskiya ce cewa idan aka fara shirya wannan tattaunawa, dole ne dukkan masu ruwa da tsaki na siyasar RD-Congo su amince cimma wata yarjejeniya. Ta wannan ne idan suka cimma yarjejeniya za a iya ganin idan, mu a bangaren gamayyar kasa da kasa, mu ga wani jadawalin aiki ya fito daga wadannan shawarwarin tattaunawa, za'a a ganin wace irin shawara ce MDD za ta dauka a wannan lokaci, in ji mista Bambara. (Maman Ada)